An kashe mutane goma a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana ci gaba kashe mutane a yayinda ake zanga zanga a Syria

Rahotanni daga Syria sun ce an kashe mutane goma a lokacin wata janaza a Homs, birni na uku mafi girma a kasar. Shedu suka ce jami'an tsaro da kuma dakarun sa-kai da ake kira Shabiha, sun bude wuta a kan a kan masu janazar, kamar yadda wani bidiyon da 'yan adawa suka saka a yana ya nuna.

Ana jana'izar ta wasu mutanen da aka kashe a cikin sa'o'i ashirin da hudun da suka wuce.

Masu kare hakkin bil'adama da masu fafitika sun ce akalla mutane hamsin ne aka kashe a Homs din daga ranar Asabar zuwa yau. Wani ma'aikacin agaji a Syriar ya ce halin da ake ciki yana dada tabarbarewa ne.