Za'a ba mazauna Legas katin shaidar zama

Gwamnatin jahar Lagos ta ce zata fara samar da katin shaidar zama ga mazauna jihar. Tuni kuma ta fara da ma'aikatan jahar.

A cewar gwamnatin Lagos din, mataki ne na neman inganta tsaro a jahar, da kuma samawa jama'a abubuwan more rayuwa.

Sai dai tuni masu sukar hakan suke ganin cewa, ba shiri ne mai dorewa ba.