Kungiyar Kwadago ta dakatar da yajin-aiki a Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

Kungiyar kwadagon Najeriya ta janye yajin-aikin gargadi na kwanaki uku da ta sha alwashin farawa a yau Laraba.

Kungiyar ta ce ta janye yajin aikin ne bayan da gwamnati ta amince da bukatarta ta biyan ma'aikata mafi karancin albashi na naira dubu goma sha takwas.

Ta ce za a fara biyan albashin daga watan Agusta mai kamawa.

Gwamnatin ta kuma amince ta biya ariyas na mafi karancin albashin ga ma'aikatan a watan Oktoba.