'Fari ya munana a kasar Somalia'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani yaro da yunwa ta galabaita a Somalia

A yau Laraba ne Majalisar Dinkin Duniya za ta bayyana cewa yanzu dai fari ya bayyana a wasu sassan kasar Somalia.

Wannan dai shi ne karon farko da yankin ya fuskanci matsalar fari cikin shekaru goma sha tara da suka gabata.

Majalisar ta ce matsalar fari, da rikice-rikice, da kuma talauci a wasu yankunan kasar, su ne suka haddasa matsalar yunwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan goma ne ke matukar bukatar agajin gaggawa a kasar.