Matsalar tabkin Chadi ga makiyaya

A yankin tafkin Chadi, makiyaya dayawa na barin kiwon suna komawa ga noma da kamun kifi, saboda wasu cututuka na kashe dabbobin nasu.

Sun zargi hukumomi da rashin taimaka masu. Amma a cewar mahukuntan, suna iya bakin kokarinsu - illa dai in dambu ne yayi yawa, ba ya jin mai.

Sai dai kuma albarkatun da ake samu daga noman na raguwa, saboda kafewar da tafkin Chadin ke cigaba da yi.

Jama'a kusan miliyan 30 ne ke amfana da tafkin Chadin a rayuwarsu ta yau da kullum.