Gwamnan babban bankin Najeriya ya gurfana a majalisa

Gwamnan babban bankin Najeriya - CBN, Malam Sanusi Lamido Sanusi, ya yiwa 'yan majalisar wakilan kasar bayani kan wasu batutuwa da bankin ya fito da su da ake cece kuce a kansu a kasar.

Batutuwan dai su ne, na rage yawan hada hada da kudi a tattalin arzikin Nigeria, na biyu kuma shine batun bankin Islama wanda ke gudanar da harkokinsa ba tare da kudin ruwa ba.

To saidai bayan da ya kammala bayaninsa, kakakin majalisar wakilan, Aminu Waziri Tambuwal, ya hana wa yan majalisar damar yiwa Gwamnan babban bankin tambayoyi.

Wannan mataki dai ya fusata wasu yan majalisar, inda suka fito daga zauren majalisar su na hayaniya da bayyana fushinsu.