Shugabannin Turai sun amince su taimakawa kasar Girka

Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa

Ga alama shugabannin Gwamnatocin kasashen da ke amfani da kudin bai-daya na Euro sun cimma wata yarjejeniya a kan irin yadda za su samar da wani gagarumin ceto domin hana tattalin arzikin kasar Girma durkushewa.

A karashin shirin bangaren yan kasuwa zai samar da euro biliyan 37 domin taimakawa kasar ta Girka.

Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya ce kafar mai zaman kanta ba za ta saka hannu a Ireland ko kuma a Portugal ba.

Ya ce, zai kasance rashin adalci idan ba a yi amfani da sauran matakai a kan Irelan da Portugala ba.

Tun farko daftarin sanarwar bayan taron,ta ce za'a ba kasashen Girka da Ireland da kuma Portugal karin lokaci na biyan basukan da ake binsu, za kuma a rage kudin ruwan da aka sa musu.