Mutum 5 sun mutu a barkewar rikici a Jos

Image caption Birnin Jos ta yi fama da rikice-rikice a baya-baya nan

A garin Jos, fadar gwamnatin jihar Plateau da ke arewacin Najeriya rikici ya sake barkewa bayan an samu zaman lafiya na wani dan lokaci a jihar.

Rahotanni sun ce kimanin mutum biyar ne suka mutu, yayin da sama da goma suka jikkata.

Batun wanzar da zaman lafiya na daga cikin alwashin da Gwamnan jihar, Jonah Jang ya yi lokacin da yake yakin neman zabe.

Sai ga shi tun tafiya ba ta yi nisa ba harkar tsaro ta fara tabarbarewa a jihar.