Lamido zai gurfana a gaban Majalisar Wakilai

Image caption Gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi

A ranar Alhamis ne ake sa ran gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi zai amsa gayyatar da majalisar wakilan kasar ta yi masa domin ya yi mata karin haske akan wasu batutuwa.

Batutuwan dai su ne sabuwar manufar da gwamnan CBN din ke shirin bullowa da su a badi domin rage hada- hada da farin kudi, da kuma karfafa cinikayya ta hanyoyin zamani.

Akwai kuma batun bada damar kafa bankin Islama, bisa tsarin da ya haramta kudin ruwa.

Batutuwan biyu dai na ci gaba da janyo kace-nace a Najeriya, inda tuni wasu shugabannin addinin Krista suka yi zargin cewa, kawo tsarin bankin Islaman wani kokari ne na tilastawa 'yan kasar su bi tsarin addinin musulunci.

Sai dai babban bankin ya sha nanata cewa batun ba shi da alaka da addini, illa dai kawai wani tsari ne da doka ta tanada.

Bankin ya kuma kara da cewa tsarin zai karfafa tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi, kamar yadda ya faru a wasu kasashen duniya.

Manyan kasashe da dama da suka hada da Burtaniya da Faransa duka na gudanar da irin wannan tsari na banki wanda ba ya ta'ammali da kudin ruwa.

Sai dai daga dukkan alamu akwai babban kalubale ga babban bankin na wayar da kan al'umar kasar musamman wadanda ba Musulmai ba domin fahimtar yadda tsarin ke aiki.