Mutane akalla 18 ne suka rasa rayukansu a zanga zangar Malawi

Shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika ya yi watsi da kiraye kirayen da ake masa na ya sauka duk da mutuwar mutane goma sha takwas din da aka samu a zanga zangar kwanaki biyun da akai ta yi ta kin jinin gwamnati.

A jawabin da yaiwa kasar, shugaba Mutharika ya ce, ba wata matsala da za'a warware da tashin hankali, kuma zai yi magana da 'yan adawa: Sai dai kuma 'yan adawar sun ce ba wani sabon abu ya ke fada ba.

Undule Mwaku-sungula yace mun gana da shugaban lokuta da dama a baya kuma bayannan ba ma ganin wani abu daga wurinsa.

Wakilin BBC da ke Lilongwe, babban birnin kasar ta Malawi, ya ce an kai hari kan gine ginen gwamnati.

Rikicin dai ya fara ne kan haushin lakadawa wasu masu fafutikar kare hakkin bil adama da wani 'yan jarida, duka.