An sabunta: 22 ga Yuli, 2011 - An wallafa a 06:12 GMT

Kungiyar al-Shabab ta mayar da martani

Kungiyar al-Shabab ta mayar da martani

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana fama da karancin abinci a Somalia

Kungiyar Musulunci ta al-Shabab a Somalia ta ce sassaucin da ta yiwa kungiyoyin bada agaji da ke aiki a yankunan da ke karkashin ikonta bai shafi kungiyoyin da ta dakatar a baya ba.

A wani taron manema labarai a birnin Mogadishu, mai magana da yawun al-Shabab Sheikh Ali Raage bai kama sunaye ko adadin kungiyoyin agajin da suka haramtawa aiki a kasar ba.

Sai dai a shekaru biyu da suka wuce al-Shabab ta haramtawa yawancin kungiyoyin agaji na Amurka da ma na Majalisar Dinkin Duniya shiga kasar.

Sheikh Ali Raage ya zargi kungiyoyin bada agajin da Majalisar Dinkin Duniya da shigar da siyasa cikin matsalar karancin abincin da ake fama da shi a Somalia, domin sanyaya gwiwar jama'a da neman shigar da su addinin Kirista.

'Dole ne mu dauki mataki'

"Kungiyoyin agajin da muka dakatar a baya ba sa cikin wannan sassaucin, ba wai yanzu ba harma nan gaba.

"Muna magana ne a kan wadanda dama suke aiki a kasar. Wasu daga cikin wadanda muka dakatar sun shiga cikin al'amuran siyasa ne. Wasu kuma na rusa rayuwar jama'armu ne. Don haka dole ne mu dauki mataki".

Sheikh Ali Raage ya kuma yi watsi da batun cewa ana fama da matsananciyar yunwa a Somalia, yana mai cewa Majalisar Dinkin Duniya na zuzuta lamarin ne, kuma ikirarin da take yi na neman agaji farfaganda ce mara tushe.

Ya ce babbar matsalar na kan Majalisar Dinkin Duniya.

"Rahoton da suka bayar na baya ya nuna cewa akwai matsalar yunwa a Somalia. Amma muka ce ba haka bane. Babu alamun gaskiya a ciki ko kadan.

"Ana fama da fari da karancin ruwan sama a Somalia, amma bai kai munin yadda suke zuzutawa ba".

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.