Sabon zargi kan jaridar News of the World

Jarimin fina-finai Jude Law
Image caption A shekara ta 2003 ne Jude law ya kai ziyara Amurka

BBC ta fahimci cewa jami'an bincike na Hukumar FBI ta Amurka na shirin tuntubar jarimin fina-finan nan Jude Law, bayanda aka yi zargin cewa an saci bayanan wayar salularsa a lokacin da ya kai wata ziyara Amurka.

An yi zargin cewa wani labari da jaridar News of the World ta wallafa a shekarar 2003 ya samo asali ne daga bayanan da aka datsa a wayar salular jarimin.

Idan aka tabbatar da wannan zargi, to zai kai ga daukar matakan shari'a a Amurka.

An yi zargin cewa masu satar bayanai sun datsi bayanan wayar salular Jude Law lokacin da ya ke filin saukar jiragen sama na Kennedy a birnin New York.

Wani labari da aka wallafa daga bisani a jaridar News of the World, ya yi bayanai dalla-dalla kan yadda jarimin ya tattauna da wani mai taimaka masa.

Rupert Murdoch ya musanta zargin

Wayar dai na amfani ne da layin Amurka, abinda kuma zai bada damar shigar da kara a karkashin tsarin shari'ar Amurkan.

Wani da ke da masaniya kan binciken ya shaida wa BBC cewa nan bada jimawa ba, jami'ai za su fara tuntubar Jude Law.

Masu magana da yawun jarimin a Burtaniya sun ki cewa komai game da batun.

Dama Hukumar FBI na bincikar wani zargi da ke cewa News of the World ta nemi samun bayanan wayoyin salular mutanen da suka mutu a harin 11 ga watan Satumba.

Sai dai a jawabin da ya yi a gaban kwamitin bincike na Majalisar Dokokin Burtaniya ranar Talata, shugaban kamfanin da ya mallaki jaridar Rupert Murdoch, ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa an saci bayanan wayoyin jama'a a Amurka.