Gwamnatin Malawi ta hana jana'izar masu zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika

Mahukunta a Malawi sun hana a gudanar da jana'izar mutanan da aka kashe lokacin zanga zangar kin jinin gwamnati da akkai ta kwanaki biyu a kasar. Iyalan mamatan na san a binne su ne a wani waje da ak fi sa ni da makabartar gwarzaye, dake arewacin birnin Mzuzu.

Sai dai kuma shugaba Bingu wa Mutharika ya umarci karamar hukumar wajen da kada su bari ai yi jana'izar.

Wani wakilin BBC a Malawi ya ce yanzu haka ana rikici tsakanin mahukuntan da iyalan mamatan.

Mutane goma sha takwas ne aka tabbatar sun mutu a lokacin da 'yan sanda sukai amfani da harsasan gaske da hayaki maisa kwalla domin tarwatsa masu zanga zanga a duk fadin kasar.