An yi jana'izar yan malawin nan bakwai

An rufe Yan Malawin nan 7 da aka kashe a wajen wata tarzomar kin jinin gwamnati a wani babban kabari a arewacin kasar bayan da dubban masu jimami sun hallara.

Hukumomin Malawi sun sauya shawararsu ta farko ta hana jana'izar mutanen .

Iyalan mamatan na son a binne su ne a wani waje da aka fi sani da makabartar gwarzaye, dake arewacin birnin Mzuzu.

Sai dai kuma shugaba Bingu wa Mutharika ya umarci karamar hukumar wajen da kada su bari a yi jana'izar.

Wani wakilin BBC a Malawi ya ce, yanzu haka ana rikici tsakanin mahukuntan da iyalan mamatan.

Mutane goma sha takwas ne aka tabbatar sun mutu a lokacin da 'yan sanda suka Yi amfani da harsasai na zahiri da kuma hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu zanga zanga a duk fadin kasar.