Bam ya tashi kusa da fadar gwamnati a Norway

Image caption Bam din ya lallata manyan gine-gine

Wani Bam ya tashi a kusa da fadar gwamnati dake Oslo babban birnin Norway.

Jami'an 'yan sanda sun ce akalla mutane bakwai ne suka mutu kuma wasu da dama sun ji rauni.

Bam din ya lallata ofishin Pira Ministan kasarm, Jens Stoltenberg, amma wata mai magana da yawun gwamnatin kasar ta ce lafiyarsa lau, kuma babu abun da ya same shi.

Babu wanda ya dauki alhakin tada bam din a kasar.

'Yan sa'o'i bayan fashewar bam din na Oslo, wani mutum da yai shigar 'yan sanda ya bude wuta kan mai uwa da wabi a wajen wani taron matasa a tsibirin Utoeya kimanin kilo mita arba'in daga arewa maso yammacin birnin na Oslo.

An ga jirage masu saukar angulu na 'yan sanda na ta tafiya tsibirin inda jam'iyyar Leba ta kasar Norwen da pira ministan ke jagoranta ta shiryawa matasa wani sansanin bada horo a lokacin hutu.