Majalisar Najeriya ta goyi bayan bankin Musulunci

Sanusi Lamido Sanusi
Image caption Wannan batu ya dade yana janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta yi na`am da shirin babban bankin kasar na ba da izinin kafa bankin da ba ya ta'ammali da kudin ruwa ko kuma bankin musulunci.

Majalisar ta cimma wannan matsayin ne bayan Gwamnan babban bankin kasar Mallam Sanusi Lamido Sanusi ya amsa gayyatar da ta yi masa.

Lamido Sanusi ya yiwa 'yan Majalisar karin haske a kan manufofin bankin a zauren majalisar.

Batun kafa bankin da ba ya ba da kudin ruwan dai ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin `yan Najeriya, inda wasu ke kallon kafa bankin kamar wani yunkuri ne na dora wa jama`a wani tsari mai nasaba da addinin Musulunci.

Hon Musa Sarkin Adar na Majalisar Wakilan ta Najeriya, ya shaida wa BBC cewa sun gamsu da bayanin da shugaban babban bankin ya yi musu.

Sannan ya kara da cewa babu wani sauyi da za su gabatar a kan dokar da ta baiwa bankin damar kafa dukkan cibiyoyin hada-hadar kudin da ya ga ta dace domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Wakilin BBC Ibrahim Isa a Abuja, ya ce babu tabbas ko amincewar da 'yan Majalisar suka yi da wannan tsari zai kawo karshen ce-ce-ku-cen da ake yi a kai.

Shi dai babban bankin na Najeriya ya ce tsarin ba shi da alaka da addini ko kadan, illa dai kawai wani bangare ne da tsarin mulkin kasar ya tanada, wanda kuma zai bunkasa tattalin arzikinta.