An haramta wa Bin Hamman shiga harkar wasan kwallon kafa

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta haramta wa shugaban hukumar kwallon kafa na yankin Asiya, Muhammad bin Hamman , shiga harkokin kwalllon kafa har tsawon rayuwarsa, bayan samunsa da laifin bada toshiyar baki.

Shugaban kwamitin da'a na hukumar ta FIFA, Petrus Damaseb, ya bayyanacewa, "jami'in Mr Bin Hammam an same shi da laifin karya tanajin doka ta uku, sakin layi na farko, da nabiyu da na uku."

Bin Hammam dan kasar Qatar, an zarge shi ne da kokarin sayen kuri'u a lokacin zaben shugaban hukumar kwallon kafar ta duniya, inda yake kalubalantar shugaban hukumar da ya dade kan mukamin, Sepp Blatter.

Mataimakin shugaban hukumar ta FIFA, Jack Warner tuni ya ajiye aikinsa, bayan zargin makamancin wannan.