Anders Behring Breivick ya gurfana a gaban Kotu

Image caption Anders Behring Breivick ya fito daga kotu a motar jami'an tsaro

Mutumin da ake zargi da kai hare haren Norway da sukayi ajalin kusan mutane dari a Oslo ya bayyana a gaban alkali.

Alkalin ya gudanar da zaman kotun ne cikin sirri saboda kada wanda ake zargin wato Anders Behring Breivick ya yi amfani da shara'ar ton tallata tsananin ra'ayinsa na rikau.

Sai dai wani lauya a kasar ta NORWAY ya shaidawa BBC cewa watakila akwai wani dalilin kuma da yasa alkalin gudanar da shra'ar cikin sirri

Ya ce; "Watakila ko alkalin yayi tutanin cewa ba'ayi nisa ba binciken da akeyi ne kuma kotun ba ta so da dauki kasadar barin jama'a da 'yan jarida su halarci shara'ar saboda tsoron ko hakan zai shafi binciken da akeyi."

Lauyan da ke kare Mr Breivick ya ce, ya amince da kai hare haren, kuma shi Mr Brevick ya ce kashe-kashen na da tada hankali, amma kuma sun zama dole.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rabon Norway da fuskar bala'i irin wannan tun yakin duniya na biyu

'Yan sanda a kasar Norway sun cesama da mutane 90 ne suka rasu a sanadiyyar wasu harbe-harbe a wani sansanin matasa dake tsibirin Utoeya a kusa da birnin Oslo, yayinda da dama kuma suka jikkata.

Ana kuma tsammanin adadin zai fi haka.

Sa'o'i biyu kafin harin, wani bam ya tashi a tsakiyar birnin na Oslo, lamarin da ya yi ajalin akalla mutane bakwai.

Wakilin BBC Richard Galpin ya ce a baya Norway bata taba fuskantar wani abu makamancin wannan ba.

Ya tsallake rijiya da baya

Wani dan bindiga sanye da kayan 'yan sanda ya bude wuta a wani sansanin matasa da ke tsibirin Utoeya a kusa da garin Oslo - daruruwan mambobin jam'iyyar Labour da ke mulkin kasar ne suka taru a wajen.

Yara da dama sun rika fadawa cikin ruwa a kokarin neman mafaka, inda a yanzu mahukunta suka ce akalla mutane 80 ne suka mutu.

Sa'o'i kadan kafin harbe-harben, wani shirgegen bom ya tashi a tsakiyar birnin Oslo, an ji karar fashewar a ko'ina cikin birnin inda ta girgiza gina-ginen gwamnati, ciki harda ofishin Fira minista.

Fira Minista Jens Stoltenberg, wanda aka nufa da harin ya tsallake rijiya da baya.

Wadanda suka ga abin da ya faru sun dimauta matuka, 'yan sanda sun shawarci Fira Ministan da kada ya bayyana inda yake lokacin da ya bayyana a gidan talabijin domin yiwa jama'ar kasar bayani.

'Muna da rawar takawa'

Shugaba Obama na Amurka ya ce harin wata matashiya ce da ke nuna cewa duniya na da rawar takawa wajen hana hare-haren ta'addanci:

"Bamu da cikakken bayani kawo yanzu, amma ina mika jimami na ga jama'ar kasar Norway, kuma wannan na tunasar da mu cewa kasashen duniya na da rawar takawa wajen hana irin wadannan hare-haren na ta'addanci afkuwa.

Ana saran Fira Ministan kasar zai halarci tsibirin na Utoeya a yau, kawo yanzu babu tabbas kan wanda ya shirya wannan harin, sai dai an kama wani mutum da ake kyautata zaton maharin ne - dan dai kasar ta Norway ne.

Kuma 'yan sanda na alakanta shi da harin bom.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar inda aka kai hare-haren