Kasar Norway na zaman makoki bayan harin jiya

Mutane 87 sun mutu a kasar Norway Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rabon Norway da fuskar bala'i irin wannan tun yakin duniya na biyu

'

Al'ummar Norway na cikin zaman makoki, kwana guda bayan kisan da aka yi wa mutane akalla casa'in da biyu, galibinsu matasa, sakamakon harbin kan mai tsautsayi da kuma harin bam.

'Yan sanda sun tuhumi wani mutum mai shekaru talatin da biyu dan kasar ta Norway, Anders Behring Breivik da aikata kisan.

Carol Soundbye, mai magana da yawun 'yan sandan Norway, ta ce, "ana zarginsa da ayyukan ta'addanci biyu. Daya a Oslo, dayankuma a Utoeya. An kuma fara yi masa tambayoyi. Ana masa tambayoyi ne kan mutuwar mutane bakwai,a dalilin tashin bam na Oslo, da kuma na mutane sama da tamanin da biyar da aka bindige a wani sansanin matasa, kusa da birnin na Oslo."

A birnin na Oslo, inda sojoji ke sintiri kan tituna, an sauko da tutoci kasa kasa, kuma mutane na ta tururuwa zuwa babbar mujami'ar birnin inda suke kunna kyandirori, suna kuma ajiye furanni.

'Yan sanda sun tabbatar cewa, mutumin da aka kama, Anders Behring Breivik, wanda ya bayyana kansa a matsayinsa mai bin addinin Kirista, kuma dan ra'ayin rikau--- ya mika kansa ne cikin ruwan sanyi, ba tare da an nemi kai ruwa rana ba. Sun ce irin bayanan da ya kan rubuta a intanet, sun nuna cewar yana da ra'ayin rikau na nuna kiyayya ga musulmi.

Ya tsallake rijiya da baya

Wani dan bindiga sanye da kayan 'yan sanda ya bude wuta a wani sansanin matasa da ke tsibirin Utoeya a kusa da garin Oslo - daruruwan mambobin jam'iyyar Labour da ke mulkin kasar ne suka taru a wajen.

Yara da dama sun rika fadawa cikin ruwa a kokarin neman mafaka, inda a yanzu mahukunta suka ce akalla mutane 80 ne suka mutu.

Sa'o'i kadan kafin harbe-harben, wani shirgegen bom ya tashi a tsakiyar birnin Oslo, an ji karar fashewar a ko'ina cikin birnin inda ta girgiza gina-ginen gwamnati, ciki harda ofishin Fira minista.

Fira Minista Jens Stoltenberg, wanda aka nufa da harin ya tsallake rijiya da baya.

Wadanda suka ga abin da ya faru sun dimauta matuka, 'yan sanda sun shawarci Fira Ministan da kada ya bayyana inda yake lokacin da ya bayyana a gidan talabijin domin yiwa jama'ar kasar bayani.

'Muna da rawar takawa'

Shugaba Obama na Amurka ya ce harin wata matashiya ce da ke nuna cewa duniya na da rawar takawa wajen hana hare-haren ta'addanci:

"Bamu da cikakken bayani kawo yanzu, amma ina mika jimami na ga jama'ar kasar Norway, kuma wannan na tunasar da mu cewa kasashen duniya na da rawar takawa wajen hana irin wadannan hare-haren na ta'addanci afkuwa.

Ana saran Fira Ministan kasar zai halarci tsibirin na Utoeya a yau, kawo yanzu babu tabbas kan wanda ya shirya wannan harin, sai dai an kama wani mutum da ake kyautata zaton maharin ne - dan dai kasar ta Norway ne.

Kuma 'yan sanda na alakanta shi da harin bom.