Yau ake zaben kananan hukumomi a jihar Sakkwato

Zabuka a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An samu tashin hankali a zabukan kasa baki daya da aka yi a bana

Masu zabe a Jihar Sokoto ta Najeriya na zaben Shugabanni da kansilolin kananan hukumomi na jihar.

Hukumar zabe ta jihar ce dai ta shirya zaben. Kuma rundunar yansandan jihar ta ce ta tanadi yansanda dubu 5 domin tabbatar da tsaro a lokacin zaben.

Wakilin BBC a yankin ya ce ana yin zaben ne cikin kwanciyar hankali ya zuwa yanzu, sai dai mafi yawancin masu zabe sun kaurace masa kuma tuni da jam'iyun adawa suka yi watsi da yadda zaben ke gudana.

A zaben da aka gudanar a baya dai, jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ce ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 23 da kuma na kansiloli 244 da jihar ke da su.

Haka kuma ta kasance a shekara ta 2004, inda jam'iyya mai mulki a wancan lokacin ta ANPP ta lashe dukkannin kujerun da aka kada kuri'a a kansu.

Abin jira a gani dai shi ne ko tarihi zai maimaita kansa a wannan lokaci ko kuma za a samu sauyi.