Zaben kananan hukumomi a jihar Sakkwato

Zabuka a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An samu tashin hankali a zabukan kasa baki daya da aka yi a bana

A ranar Asabar ne al'ummar jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ke fita domin kada kuri'a a zabukan 'yan Majalisun kananan hukumomi a jihar.

Tuni dai hukumar zaben Jihar da kuma Jam'ian tsaro suka ce sun kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da zabukan yadda ya kamata.

Amma wasu masu zabe a Jihar sun shaida wa wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza cewa za su kauracewa zaben.

Da dama daga cikinsu sun koka ne kan yadda ba a gudanar da zabe mai inganci a kasar.

Amma duk da haka wasu masu zaben sun ce za su fita domin zabar shugabannin da za su inganta rayuwarsu.

A zaben da aka gudanar a baya dai, jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ce ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 23 da kuma na kansiloli 244 da jihar ke da su.

Haka kuma ta kasance a shekara ta 2004, inda jam'iyya mai mulki a wancan lokacin ta ANPP ta lashe dukkannin kujerun da aka kada kuri'a a kansu.

Abin jira agani dai shi ne ko tarihi zai maimaita kansa a wannan lokaci ko kuma za a samu sauyi.