An kashe shugaban yan tawayen Sudan ta Kudu

An kashe wani jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu, wanda ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar sulhu da gwamnati, a wani yanayi na matukar jayayya.

'Yan kungiyar Gatluak Gai sun ce gwamnati ce ta yi masa gadar-zare ya fada, aka kuma bindige shi.

Ita kuma gwamnatin Sudan ta Kudu cewa take mutanensa ne suka kashe shi.

Shi dai Kanar Gai dan kabilar Nuer ne, wadda ke jayayya da kabilar Dinka, wadda ita ce mafi rinjaye a Sudan ta Kudu.