Makashin jama'ar nan a Norway ya ce shi kadai ya aikata ta'asar

Masu nuna alhini game da kashe kashen jama'a  a Norway Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu nuna alhini game da kashe kashen jama'a a Norway

Mutane kusan dari ne dai ake kyautata zaton sun mutu a harin kan mai tsautsayi, da kuma na bam da aka kai ranar Juma'a kasar Norway.

'Yan sanda sun ce mutumin da suke tuhuma da aikata laifukkan biyu, Anders Behring Breivik ya shaida masu cewa shi kadai ya aikata hakan.

Geir Lippestad , lauyan Mr Breivik, ya ce, "abinda yake fadi shi ne cewar yana son kawo sauyi a cikin al'umma, kuma a tunaninsa, hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar juyin juyahali."

Dan bindigar ya harbe mutane akalla tamanin da biyar a wani tsibiri, yayinda akwai wasu mutanen biyar da ba aji duriyarsu ba. Mutane bakwai ne kuma suka mutu a birnin Oslo sakamakon tashin bam na mota.

Haka kuma yayinda ake ci gaba da bincike kan hare haren na ranar Juma'a, jama'a kasar ta Norway na ci gaba da makokin abin da ake bayyanawa da hari mafi muni da kasar ta fuskanta, tun bayan yaki duniya na biyu.

Jami'an gwamnati da kuma 'yan gidan sarautar kasar ta Norway sun halarci wani taron addu'o'i na musamman a babbar mujami'ar birnin Oslo.

Da dama daga cikin wadanda suka hallara sun rika zubar da hawaye, haka nan kuma a wani jawabi mai sosa rai, Pirayim minista, Jens Stoltenberg ya bayyana kisan mutanen a matsayin wata masifa.

Shi ma a jawabin da ya gabatar a birnin Roma, Paparoma Benedict ya bayyana alhininsa, sannan ya kuma bukaci jama'a da su kauce ma hanyar da ya kira ta nuna kiyayya.

Tuni dai an samu karin haske kan ko wanene Anders Behring Breivik, mutumin da ake zargi da kai hari a kasar Norway. Ya bayyana cewa yana da ra'ayin rikau na kin jinin musulunci.

Wadanda suka bi diddigin rubuce-rubucensa a shafin intanet ma, sun ce yana da tsattsauran ra'ayin siyasa. Mutumin wanda kafafan yada labarai suka bayyana da suna Anders Behring Breivik, ba shakka dan kasar Norway ne, baya ga yadda yake zaune a cikin jama'a, 'yan sanda sun ce kalaman da ya wallafa a intanet na baya-bayan nan sun nuna cewa yana da ra'ayin rikau na kin jinin musulunci.

Hans Ferguson wani dan jarida da ke aiki da jaridar Pigi:

"Na gayawa mutane cewa mutumin da ake zargin yana da rikakkiyar adawa da gwamnatin jam'iyyar Labour, kan abin da ya ke gani kamar sakaci ne wajen fuskantar kungiyoyin musulmai.

Amma ina ganin babu wanda zai goyi bayansa akan wannan aika-aikar.

Kirista ne mai tsattsauran ra'ayi

Ya bayyana a shafinsa na Facebook wanda yanzu aka cire daga intanet, cewa shi kirista ne mai tsattsauran ra'ayi.

Ya taso ne a birnin Oslo, sannan ya fita domin kafa gonar lambu.

Wani da ake wa kallon karamin manomi, yanzu ya ce ya sayi ton shida na sinadarin taki - wanda ake amfani da shi wajen hada bom.

A yanzu 'yan sandan Norway sun ce mutumin da suke zargin ya amsa wasu daga cikin abubuwan da ake zarginsa da aikatawa.

Babban abin tambayar shi ne dalilin da ya sanya shi yin abinda ya yin? Da kuma ko yana aiki ne tare da wasu gungun jama'a da ke shirin kaddamar da makamantan wannan hari a gaba.