An kashe fararan hula a Maiduguri

Kungiyar kare hakkin bil`adama ta Amnesty International ta zargi jami`an rundunar hadin-gwiwa da tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno da kashe akalla farar-hula ashirin da shida.

Kungiyar ta ce ranar asabar din da ta gabata ne jami'an tsaron JTF din suka kashe mutanan a wasu harbe-harben da suka yi na kan-mai-uwa-da-wabi bayan tashin wani bom a kasuwar Budum da ke garin Maiduguri.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta hana jami`an tsaronta yi wa al`uma kisan-gilla a jihar.