An gurfanar da Anders Breivik cikin sirri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Anders Behring Breivik ya kashe sama da mutane 90

Mutumin da ake zargi da kai hare haren Norway da sukayi ajalin kusan mutane dari a Oslo ya bayyana a gaban alkali.

Alkalin ya gudanar da zaman kotun ne cikin sirri saboda kada wanda ake zargin wato Anders Behring Breivick ya yi amfani da shara'ar ton tallata tsananin ra'ayinsa na rikau.

Sai dai wani lauya a kasar ta NORWAY ya shaidawa BBC cewa watakila akwai wani dalilin kuma da yasa alkalin gudanar da shra'ar cikin sirri

Ya ce; "Watakila ko alkalin yayi tutanin cewa ba'ayi nisa ba binciken da akeyi ne kuma kotun ba ta so da dauki kasadar barin jama'a da 'yan jarida su halarci shara'ar saboda tsoron ko hakan zai shafi binciken da akeyi."

Lauyan da ke kare Mr Breivick ya ce, ya amince da kai hare haren, kuma shi Mr Brevick ya ce kashe-kashen na da tada hankali, amma kuma sun zama dole.

'Yansandan suna ci gaba da nazari akan jadawalin da ya wallafa a Internet ranar da ya kai harin.

Sun ce suna ci gaba da tattaro bayanan da ke yin karin haske a kan mutumin.

Kalaman da ya rika yi na nuna adawa da shigowar baki Musulmi kasar ta Norway da kuma abin da ya kira bijirewa asali da Turawa ke yi za su taimaka wajen ba da haske a kan tunaninsa da kuma yadda yake kallon al'amari.

Jama'ar Norway sun sunyi tsit na minti guda don tunawa da wadanda aka kashe ranar juma'a.

Prime Minista da sarkin kasar ne suka jagoranci dubban jama'a a wani bikin nuna alhini da aka gudanar a wajen jami'ar Oslo.