Ba laifin da nai! Inji Anders Behring Breivik

Anders Behring Breivik Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mutumin da ya kai hari a Norway

Fiye da mutene dubu dari ne suka taru a tsakiyar Oslo babban birnin Norway, don tunawa da wadanda suka mutu a harinda aka kai ranar juma'a, harin da ya yi ajalin mutane saba'ain da shidda.

Yawancin mutanen da suka taru din dai na rike da furanni, suna rungumar juma cikin wani yanayi mai sosa rai.

Yanzu dai 'yan sanda na gudanar da bincike don gano ko da hannun wasu a cikin harin, bayan wanda ya kai harin ya ce ba shi kadai ya kitsa shirya shi ba.

Mr Breivik ya ce tabbas shi ne ya kai harin, amma ya ki amsa laifin aikata ta'addanci