Matsalar bashin Amurka

Image caption Shugaba Obama da kakakin Majalisar Wakilan Amurka

Shugaba Obama da daya daga cikin manyan abokan adawarsa na jam'iyyar Republican, John Boehner, sun bayyana mabambantan ra'ayoyinsu dangane da matsalar bashin da Amurka ke fama da ita kai tsaye ta akwatin talabijin.

A cewar Mista Obama, za'a yiwa tattalin arzikin kasar mummunar illa muddin ba a cimma yarjejeniya ba kafin cikar wani wa'adi nan da mako guda.

Shugaban ya dora laifi akan yan majalisar wakilan jam'iyyar adawa ta republicans da tsayawa akan abun da ya kira matakin da ya ji kowane bangare wurin magance matsalar gibin Amurka.

Sai dai ya ce ba zai yadda jama'ar Amurka su kasance wadanda zasu fi jin jiki a rikicikin siyasar kasar ba.

To sai dai a nasa bangaren shugaban yan majalisar wakilan Amurka John Boehner ya zargi shugaba Obama da yin baki biyu akan tattaunawar baya bayanan da kuma bulo da wani yanayi na rikici.

Jawabin da suka gabatar ta kafar talibijin na nuni dacewa al'amura sun kara tababbarewa dangane da matakin da ya kamata a dauka domin shawo kan matsalar bashin kasar.