Burtaniya ta amincewa Gaddafi ya ci gaba da zama a Libya

Image caption William Hague

Burtaniya ta bi sahun Faransa wajen nuna amincewa da shawarar cewa shugaba Gaddafi na Libya ka iya ci gaba da zama a kasarsa in har zai sallama dukkan ikon da ya ke da shi.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, William Hague, ya ce Burtaniya za ta fi so Kanar Gaddafi ya fice daga Libya, amma shawara ta karshe ta rage ga al'ummar kasar.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman ga ksar Libya, Abdelilah Al-Khatib, ya ce shi ma ya yi amanna al'ummar kasar Libya ne ke da magana ta karshe a kan makomar Kanar Gaddafi.

Ya ce muna san cewa duk wata tattaunawa dangane da makomar shugabannin wata kasa al'amari ne da ya shafi al'ummarsu.

Don haka tattaunawa dangane da ko Kanar Gaddafi zai ci gaba da zama a cikin kasar alhaki ne na mutanen kasar.

'Yan adawar kasar ta Libya dai sun nuna cewa Kanar Gaddafi ka iya ci ci gaba da zama a kasar idan ya sauka daga mulki.