An fara kai agajin abinci Somalia

Image caption Sama da mutane miliyan 11 ga bukatar agajin abinci

An dan anjiman nan ne Jirigin saman farko na Hukumar samarda abinci ta Majalisar Dinkin Duniya zai isa babban birnin Somalia wato Mogadishu.

Wannan na ciki yunkurin kasashen duniya na samarda da agaji ga wajen sama da mutane miliyan goma dake fama da fari a gabashin kusurwar Afrika.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kimanin mutane dubu arba'in ne suka isa Mogadishu a 'yan makwannin da suka gabata, wadanda kuma galibi ke matukar bukatar abinci, ruwan sha da kuma matsuguni.

Akwai kuma `karin wasu mutanen dubu talatin da suka isa wasu sansanonin dake birnin.

A lokacin da jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ziyarci daya daga cikin sansanonin a jiya litini, kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijirar Vivian Tan ta ce yaga yadda mutane ke ci gaba da karuwa.

"Abin daya ganin shine tarin jama'a a fusace wadanda ke fama da yunwa a wuraren da ake rarraba kayan abincin,"

"Mutane nata turereniya, yayin da wasu kuma ke ta ribibin kwasar kayan abincin, kuma muna fargabar cewa wadanda basu da karfin kutsawa ba za su iya samun komai ba." In ji Vivian Tan Kai kayayyakin agaji zuwa Mugadishu dai zai taimaka wajen rage irin wannan yanayi, sai da ba zai magance matsalar baki daya ba na yadda za'a iya kai kayan abinci zuwa Shabelle da kuma Bakool.

Kuma matukar hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya bata iya kaiwa ga wadannan wuraren ba, mutanen dake fama da yunwa za su ci gaba da ficewa daga Mugadishu, inda ma'aikatan agaji da dama ke fargabar cewa mutanen zasu iya mutuwa akan hanya.