'Yan jam'iyyar Republicans zasu kada kuri'a kan bashi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kakakin Majalisar Wakilan Amurka John Boehner

Shugabannin jam'iyyar Republicans a Majalisar dokokin Amurka sun jinkirta kada kuri'a me muhimanci game da shirinsu na kaucewa gazawa wurin biyan basussukan da ake bin kasar.

'Yan jam'iyyun Republicans da Democrats a Majalisar sun gabatar da shirye-shiryen da suka yi hannun riga da juna don kayyade yawan basussukan da gwamnati za ta iya karba da kuma rage gibin kasafin kudin kasar.

'Yan jam'iyyar Republicans sun shirya kada kuri'a kan batun yau Laraba, sai dai masu bincike a majlisar dokokin kasar sun ce akwai tambaya kan alkaluman da suka fitar.

Shugabannin jam'iyyar Republicans zasu gabatar da wani shirin dage dokar data kayyade yawan bashin da gwamnati zata iya karba ta hanyar samar da kudi dala trilion daya da digo biyu domin zaftare yawan kudaden da za'a kashe fiye da shekaru goma masu zuwa.

Sun ce kudaden da za'a zaftare sun kai zunzurutun kudi dala biliyan dari takwas da hamsin , sai dai adadin yayi kadan.

Yanzu dai shugabannin sun dage ranar da zasu kada kuri'ar har zawa gobe alhamis yayinda zasu sake yin nazari akan shirin.

Sai dai yayinda ya ragewa kasar kwanaki shida ta fuskanci yuwar gazawa wurin biyan basusukan da ake binta shugaba Obama na kokarin ganin hakan be faru ba .