'Babu wata alaka tsakanin Ingila da Breivick'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an Yansanda a Norway

Shugabar hukumar 'yan sandan ciki ta Norway ta ce ya zuwa yanzu, ba a samu wata kwakkwarar hujja ba da ke nuna cewa akwai alaka tsakanin mutumin da ake zargi da kai hare-haren ranar Juma'a da kuma wasu masu tsattsauran ra'ayi a Burtaniya

Sai dai shugabar 'yan sandan cikin, Janne Kristiansen, ta ce ko da ya ke ana ci gaba da bincike, ta yi amanna shi kadai ya shirya hare-haren da suka yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla saba'in da shida.

Sai dai Breivik da kansa ya rubuta cewa ya halarci tarurukan da aka gudanar a Birtaniya a shekaru tara da suka wuce da kuma zanga zangar da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi a Birtaniya suka gudanar a bara.

Sakamakon hare haren da aka kaiwa kasar shugabar hukumar ta ce za'a yi nazari akan harkar tsaron kasar Norway.