Batun karbar bashi a Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barack Obama

'Yan majalisar wakilan Amurka na jam'iyar Republican da takwarorinsu na jam'iyar Democrat sun gaza sasantawa game da batun bashin da kasar za ta iya karbowa.

'Yan majalisar sun tafka zazzafar muhawara game da batun a jiya Alhamis sai dai sun kammala zaman majalisar ba tare da cimma matsaya ba.

Su dai 'yan majalisar na bangaren jam'iyar Republican suna so ne a takaita adadin bashin da kasar za ta iya karbowa.

Shi kuma Shugaba Barack Obama da 'yan jam'iyarsa ta Democrat suna so ne kada a takaita yawan bashin da za su karbo.

Idan dai ba a sasanta game da batun ba kafin ranar Talata mai zuwa, Amurka na iya fadawa cikin mawuyacin yanayin tattalin arziki.

Sai dai wadansu 'yan majalisar sun bayyana kwarin gwiwarsu wajen ganin an shawo kan batun kafin wa'adin ya cika.