Ranar yaki da cutar ciwon hanta ta duniya

Image caption Yadda ake gwaji domin sanin ko mutum na dauke da ciwon hanta

Yau ce ranar yaki da cutar ciwon hanta ta duniya, kuma hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya ta ce mutane da dama ne ke dauke da wannan cuta wadda a Turance ake kira Hepatitis, amma ba tare da sun sani ba.

Alkaluma sun nuna cewa, miliyoyin mutane ne cutar ta Hepatitis ke hallakawa a fadin duniya.

An dai ware wannan rana ne domin jawo hankali ga illar wannan cutar, da kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin shawo kanta.

Dokta Mansur Kabir, shi ne daraktan kula da lafiyar al'umma a ma'aikatar lafiya ta Najeriya, kuma ya ce hanyoyin da ake kamuwa da cuttar sun hada ta juma'i, ko marasa lafiya da ake dorawa jinin dake dauke da kwayar cuttar ko wurin yin alurai.

Ya kuma ce mata masu juna biyu da dauke kwayar cuttar idan ba'a dauki mataki ba su kan iya ba 'yayansu dake ciki.