Mutane na darin-darin komawa gidajensu a Ivory Coast: inji Amnesty

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Alasan Quattara

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty international ta ce wani yanayi na tsaro a Ivory Coast ya hana mutane fiye da rabin miliyan komawa gidajensu, watanni bayan tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugabn kasar da aka gudanar, wadanda kuma suka yi sanadiyyar asarar daruruwan rayuka.

Wani rahoto na kungiyar ta Amnesty ya ce ana zargin wasu mayakan sa-kai masu biyayya ga sabon shugaban kasar, Alassane Ouattara, da kashe-kashe mutane ba bisa ka'ida ba, da kuma ganawa magoya bayan abokin adawarsa, Laurent Gbagbo, ukuba.

Da ya ke magana a birnin New York na Amurka, Shugaba Ouattara ya yi alkawarin cewa za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a tashe-tashen hankula, ko da kuwa mai goyon bayansa ne

Rahoton ya yi kira ga shugaba Quattara da ya rusa kungiyoyin sa- kai masu yi masa biyaya .