Libya: 'Mai yiwuwa NATO ta yi karan-tsaye ga takunkumi'

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ko Kwamitin Tsaro zai dauki mataki a kan kasashen NATO?

An samu baraka a cikin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya a yau game da Libya, inda Jakadan Afrika ta Kudu ya yi gargadin cewa masu goyon bayan yan tawaye na cikin hadarin keta takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta saka wa kasar.

Yana magana ne kwana daya bayan Birtaniya ta amince da ‘yan tawayen ta fuskar difilomasiya, ta kuma ce za ta mika masu kudin gwamnatin Libyar da ta hana ta tabawa.

Hakan na zuwa ne dai a lokacin da yantawayen suka ce sun kwace iko a wasu kananan garuruwa uku, a kusa da kan iyaka da Tunisia, a wani abun da suka bayyana a matsayin gagarumin farmaki a kan dakarun Kanar Gaddafi.

'Yan tawayen Libya sun ce sun kwace wasu kanana garuruwa uku da ke kusa da kan iyakar Tunisia, a wani abu da suka kwatanta a matsayin babban hari da suka kai kan dakarun kanal Gaddafi.

An yi ta jin harbe-harbe a wasu garuruwa da ke kusa da wajen.

‘Yan tawayen sun ce su kusan dari biyar ne suka kai harin.

Wakilin BBC ya ce an ambato wani kakakin 'yan tawayen na cewa suna ta harbi da manyan bindigogo da tankunan yaki a kan dakarun gwamnati da ke amfani da garin a matsayin wani sansani.