An rantsar da sabon shugaban Peru

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ollanta Humala

An rantsar da sabon shugaban kasar Peru, Ollanta Humala, inda ya yiwa talakawa alkawarin bunkasa tattallin arzikin kasar.

A bikin rantsarwar da aka gudanar a jiya Alhamis, shugaban kasar ya ce zai gudanar da mulki ne a matsayin shugaba mai matsakaicin ra'ayi.

Ya nada majalisar zartarwa da ta kunshi masu sassaucin ra'ayi.

Mista Humala ya yi alkawarin kawo tsare- tsare masu sauki ta fuskar kasuwanci, tare da magance matsalar bambance-bambance, da cin hanci da rashawa.