Sarkin Musulmin Najeriya ya yi jawabi game da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa

A Najeriya,Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya nuna damuwa game da yadda gwamnati ke amfani da jami'an tsaro wajen kokarin warware matsalar Boko Haram da tafi kamari a jihar Borno.

Sarkin Musulmin dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron sarakuna da malamai da aka gudanar jiya Alhamis a Kaduna.

Ya ce suna yin bakin kokarinsu wajen ganin an tabbatar da adalci game da mutanen da gwamnati ta kama, wadanda take zargi da kasancewa 'yan kungiyar Boko Haram.

Wannan dai shi ne karon farko da Sarkin Musulmin ya yi tsokaci akan rikicin na Boko Haram.