Abou Diaby zai yi jinya na makwanni 10

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Diaby ya takawa Arsenal leda so 20 a kakar wasan bara

Dan wasan Arsenal Abou Diaby ba zai samu taka leda ba a farkon kakar wasan bana, saboda tiyatar da aka yi mishi a idon sahun sa.

Diaby, mai shekarun haihuwa 25, ya yi ta fama da rauni a karshen kakar wasan bara, kuma baya tare da sauran tawagar kungiyar da suka wasan sada zumunci na a Asiya da kuma Jamus.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce Diaby ba zai samu taka leda ba a wasan da kungiyar za ta buga da Newcastle da Liverpool da kuma Manchester United.

"Ina ganin zai dawo nan da makwanni takwas wato wauraren karshen watan Augusta kenan." In ji Wenger.