Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Zazzabin cizon sauro

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO a duk shekara mutane miliyan 500 ne ke kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro kuma abinda ke kaiwa ga mutuwar mutane miliyan daya duk shekera.

Yayinda kimanin kashi 86 cikin dari na mutuwar ana samunta ne a kasashen Afrika ta kudu da Sahara.

Haka kuma an kiyasta cewa kimanin yara dubu uku ne ciki har da jarirai ke mutuwa a kullum, yayinda mata masu juna biyu dubu goma ne kuma ke mutuwa daga zazzabin cizon sauro duk shekara a nahiyar Afrika.

Hukumar dai ta nuna cewa zazzabin cizon sauro ya fi addabar talakawa, inda kashi sittin cikin dari na cutar ke kama kashi ashirin cikin dari na mutanen da suka fi fama da talauci a duniya.

Wani binciken da asusun talafawa yara na Majalisar dinkin duniya wato Unicef ya gudanar ya ce a kowani dakikoki talatin yaro daya na mutuwa a duniya sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro.

Asusun ya ce zazzabin cizon sauro na daya daya daga cikin cuttukan dake yiwa yara illa har ma ya kai ga mutuwa musaman idan ya hada da talauci, abun da ya yiwa kasashe masu tasowa katutu.

Hakazalika asusun ya ce zazzabin cizon sauro ya fi shafar yara dake kasa da shekaru biyar kuma kashi goma cikin dari na mace macen yara a kasashe masu tasowa na faruwa ne sakamakon kamuwa da cutar.

Asusun ya kuma ce gwamnatocin kasashen Afrika na kashe dala biliyan goma har zuwa goma sha biyu a kowace shekera domin yaki da cutar.

A shekerar 2000 ne kuma gwamnatocin wasu kasashen Afrika su ka yi alkawarin aiwatar da wasu jerin matakan yaki da cutar kafin karshen shekarar 2005 ta hanyar amfani da gidan tsoro ga kashi sittin cikin dari na mutanen dake fuskantar barazana wurin kamuwa da cuttar da kuma samar da magunguna ga kashi sitin cikin dari na mata masu juna biyu.

Sai dai za'a iya cewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba ganin yadda har yanzu kanana yara da mata masu juna biyu na cigaba da fuskantar wannan matsala ta zazzabin cizon sauro.