Majalisar dattawan Amurka ta yi watsi da kudurin doka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dattawan Amurka

Majalisar dattawan Amurka ta yi watsi da kudirin dokar da majalisar wakilan kasar ta amince da shi na neman a `dan kara adadin basussuka da kasar za ta iya karba.

Tun da farko dai an yi zaton aukuwar hakan a kuri'ar da 'yan majalisar dattawan suka kada, inda jami'iyar Democrat ke da rinjaye.

Hakan dai ya ba da damar ci gaba da tattaunawar da za ta kai ga cimma matsaya game da batun.

Da ya ke jawabi bayan da 'yan majalisar dattawan suka kammala kada kuri'a, shugaban masu rinjaye a majalisar, Harry Reid, ya bukaci takwararsa na jam'iyar Republican Mitch McConnell, ya sake dubu bukatar 'yan jam'iyar Democrat din da idon basira.

Idan dai majalisun biyu basu samu matsaya game da batun ba, kasar na iya fuskantar tsaiko a fannin tattalin arzikinta.