Matsalar tsaro a Iraki. Gara jiya da yau

Wani rahoto da babban jami'in Amurka mai sa ido kan aikin sake gina Iraki ya fitar na gargadin cewa harkar tsaro a Irakin na ci gaba da tabarbarewa, kuma a yanzu matsalar rashin tsaron ta fi muni in aka kwatanta da bara.

An fitar da rahoton ne yayinda Amurkar ke shirin janye ragowar sojojinta, dubu arba'in da bakwai daga Irakin, nan zuwa karshen wannan shekara, duk kuwa da fargabar da ake yi cewar jami'an tsaron Irakin da wuya in zasu iya tabbatar da cikakken tsaro a halin da ake ciki.