NEMA ta gano jirgin saman da ya fadi a Osun

Ma'ikatan NEMA na aikin ceto Hakkin mallakar hoto nema
Image caption Ma'ikatan NEMA na aikin ceto

Hukumar bada taimakon gaggawa a Nigeria NEMA, ta ce ta gano inda wani jirgin sama mai saukar ungulu ya fadi a wani kauye dake jihar Osun.

Dukkanin mutanen dake cikin jirgin guda uku sun rasu wadanda suka hada da mata guda biyu da kuma matukin jirgin.

Jirgin saman mai saukar ungulu na wani kamfani mai zaman kansa, ya fadi ne a jiya da rana, amma sai da safiyar yau ne aka gano inda ya fadi.