An harbe mutane goma sha daya a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wadansu mutane da suka rasa iyalansu sakamakon hari a Pakistan

An harbe har lahira mutane goma sha daya a garin Quetta na kasar Pakistan.

Ana dai kyautata zaton cewa dukkanin mutanen 'yan Shia ne wadanda basu da rinjaye a tsakanin musulmai a kasar.

Jami'an 'yan sanda sun ce wasu mutane ne dauke da bindigogi da ba a san ko su wanene ba, suka bude wuta akan wata mota kusa da tashar motocin bos, inda kuma suka raunata mutane da dama.

Garin Quetta dai shi ne babban birni a jihar Baluchistan da ke da iyaka da Afghanistan.

A wani bangaren kuma, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanya takunkumi akan 'yan kungiyar Taliban a Pakistan wadanda ake zargi da kai hare-haren da suka yi sanadiyar mutuwar daruruwan 'yan kasar.