An nada sabon shugaban sojojin Turkiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firayim Ministan Turkiya, Tayyip Erdoga

Gwamnatin Turkiya ta nada sabon shugaban rundunar sojojinta, sa'o'i bayan murabus din da manyan kwamandojin sojinta hudu suka yi.

A jiya Juma'a ne dai sojojin wadanda suka hada da babban hafsan sojojin kasar suka sauka daga kan mukamansu.

Sun ajiye aiki ne don nuna adawarsu da shari'ar da ake yi wa wasu jami'an rundunar sojin kasar.

Wata sanarwa daga ofishin Firayim Ministan ta ce sojojin kasar za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa don kawo hadin kan kasar.