Gwamnati za ta tattauna da 'yan kungiyar Boko Haram

Image caption Mohammed Yusuf

A Najeriya, gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zai tattauna da kungiyar Boko Haram da zummar dakatar da hare-haren da 'yan kungiyar ke kaiwa a wasu sassan kasar.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayyar kasar ta ce a ranar Talata ne za a kaddamar da kwamatin, wanda ya kunshi ministoci guda shida da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin tsaro.

Gwamnatin ta kara da cewa ta yi matukar damuwa da yawan hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa shi ya sanya take son ganin ta kawo karshensa ta hanyar sasantawa da 'yan kungiyar.

Hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram da kaiwa dai sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasar musamman a jihar Barno inda anan ne suka fi tasiri.