An kashe mutane akalla 80 a rikicin Syria

Dakarun Syria
Image caption Dakarun Syria

Rahotanni daga Syria sun ce akalla mutane tamanin sun rasu, da dama kuma sun jikkata sakamakon wani hari a birnin Hama.

Tankoki yaki sun danna cikin birnin daga kafofi daban-daban da sanyin safiya, suna yin fatali da shingayen da masu zanga-zanga suka kafa.

'Yan adawa sun ce an kai samame da dama a garuruwan Dier el Zoor dake gabashi, da kuma birnin Dera'a dake kudancin kasar.

Rahotanni sun ce sojoji sun kama birnin Moadamiya, sannan an katse wutar lantarki da harkokin sadarwa.