AU zata yi taro kan yunwar Somaliya

Tarayyar Afrika ta bayar da sanarwar cewa zata gudanar da taro na musamman domin neman taimako ga wadanda fari ya shafa a Somalia, wanda majalisar dinkin duniya ta ce ya jawo asarar rayuka dubu goma.

Wannan kalami ya fito ne bayan kafafen yada labarai a Afrika sun soki kungiyar da nuna halin ko in kula.

Mataimakin shugaban Tarayyar Afrikan, Erastus Mwencha ya ce wannan taro zai hada kan shugabannin kasashe da kuma sauran kasashen duniya.

Sai dai ba a saka da ranar gudanar da wannan taro ba.