An kashe mutane sama da dari a Syria

Rikici a kasar Syria
Image caption Rikici a kasar Syria

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce ya girgiza da abinda ya kira zaluncin da gwamnatin Syria ta ke yi wa jama'arta.

Wadannan kalamai sun biyo bayan daya daga cikin ranaikun da aka fi zub-d- jini, tun bayan da aka fara rikicin a tsakiyar watan Maris.

An kashe akalla mutane dari a sassa daban-daban na kasar, sakamakon harin da gwamnati take kai wa 'yan adawa.

Yawancin wadanda suka rasa rayukan nasu suna birnin Hama ne, wanda jami'an soja suka durfafa da sanyin safiya, inda aka ce an kashe mutane sama da saba'in.