Syria: Sojoji sun kaddamar da hare-hare a Hama

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun sojin Syria

Sojojin kasar Syria sun kaddamar da hare-hare a birnin Hama, daya daga cikin biranen da aka gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Dakarun sojin sun fada garin ta kowacce kusurwa da sanyin safiyar yau Lahadi.

Wasu mazauna birnin sun shaidawa BBC cewa sun yi ta jin harbe-harben bindigogi, kana wani mutum a Hama, ya ce an samu rahotannin da ke cewa an kashe mutane goma, yayin da wasu mutanen da dama suka samu raunuka.

Wani likiti ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa tankokin yaki sun yi ta luguden wuta a birnin, kuma asibitin da ke ba da magani ga wadanda suka samu raunuka na fuskantar karancin jini.