Zanga zangar nuna kyamar cin hanci a Indiya

Zanga zanga a Indiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zanga zanga a Indiya

Dubban magoya bayan dattijon nan dake fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a India, Anna Hazare, sun yi cincirindo a wajen gidan kurkukun da aka daure shi a birnin Delhi a jiya Talata.

Duk da cewa hukumomin kasar ta India sun bada umurnin a sake shi, amma Anna Hazare ya ce ba zai fita daga kurkukun ba, har sai mahukunta sun ba shi damar cigaba da yin yajin cin abincin da ya shirya gudanarwa gabannin a kama shi.

Yanzu haka dai ana gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Mr Hazare a duk fadin kasar ta India.

Tun farko, Praministan Indiyar, Manmohan Singh, ya yi kakkausar suuka ga Mr Hazare, kuma ya ce wajibi ne masu zanga-zanga su mutunta doka.